Jihar Kaduna na bukatar $95bn domin ta gyara ayyukan cigaba - El-Rufai

Jihar Kaduna na bukatar $95bn domin ta gyara ayyukan cigaba - El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai yace jihar na bukatar N95bn don ta gyara ayyukan cigaba a jihar daga nan zuwa shekara 30

- Gwamnan ya bayyana hakane a wani taron masu hannun jari a jihar Kaduna, inda tsohon shugaban kasar Tanzania, Dr. Jakaya Kikwete yayi kira ga ‘yan Afirika dasuyi kokarin bunkasa tattalin arzikinsu

- El-Rufai yace gwamntinsa ta kawowa jihar cigaba da jari da aka zuba a jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai yace jihar na bukatar N95bn don ta gyara ayyukan cigaba a jihar daga nan zuwa shekara 30 masu zuwa.

Gwamnan ya bayyana hakane a wani taron masu hannun jari a jihar Kaduna, inda tsohon shugaban kasar Tanzania, Dr. Jakaya Kikwete yayi kira ga ‘yan Afirika dasuyi kokarin bunkasa tattalin arzikinsu saboda hakan ne zai jawo hankalin masu zuba hannun jari.

Jihar Kaduna na bukatar $95bn ta gyara ayyukan cigaba - El-Rufai

Jihar Kaduna na bukatar $95bn ta gyara ayyukan cigaba - El-Rufai

El-Rufai yace gwamntinsa ta kawowa jihar cigaba da jari da aka zuba a jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata, wanda 79% na jarin da aka zuba daga kasashen waje ne.

KU KARANTA KUMA: Sanata Jang zaiyi karar Lai Mohammed akan sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati da ya bayyana

Gwamnan ya kara da cewa suna bukatar yin ayyukan ne wanda daga yanzu zuwa shekara 2050, yace “munaso mu inganta fannonin Ilimi, Lafiya, Hanyoyi, Ruwa, da kuma Noma a jihar”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel