Nigerian news All categories All tags
Sanata Jang zaiyi karar Lai Mohammed akan sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati da ya bayyana

Sanata Jang zaiyi karar Lai Mohammed akan sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati da ya bayyana

- Tsohon gwamna kuma yanzu Sanata mai wakiltar Plateau ta Arewa Jonah Jang yace zaiyi karar Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed akan yadda ya bayyana cewa ya dauki N12.5bn

- Sanatan yace yana mamakin yanda akace ya samu irin wadannan makudan kudi ba tare da an bayyana hannun wanda ya samesu ba

- Sanatan ya kara da cewa kafin ya zama sanata iya iya kokarinsa don ya kyautatawa mutanensa amma gwamnatin APC ta dage akan cewa sai ta bata masa suna ta ko wace hanya

Tsohon gwamna kuma yanzu Sanata mai wakiltar Plateau ta Arewa Jonah Jang yace zaiyi karar Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed akan yadda ya bayyana cewa ya dauki N12.5bn, kuma ya zama abun dariya a gareshi.

Sanatan yace yana mamakin yanda akace ya samu irin wadannan makudan kudi har N12.5bn ba tare da an bayyana a hannun wanda ya samesu ba, saboda duk wanda akace ya saci kudi sai an bayyana inda ya samesu.

Sanata Jang zaiyi karar Lai Mohammed akan sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati da ya bayyana

Sanata Jang zaiyi karar Lai Mohammed akan sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati da ya bayyana

Sanatan ya kara da cewa kafin ya zama sanata iya iya kokarinsa don ya kyautatawa mutanensa amma gwamnatin APC ta dage akan cewa sai ta bata masa suna ta ko wace hanya don ganin cimma gurinsu akaina.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai isa ya kashe $1bn wajen siyan makamai ba har sai mun amince da hakan – Sanata Ben Bruce

Ya bukaci Ministan da “ya gaggauta canza maganganun da yayi akasa kafin wani dan lokaci kalilan, idan kuma yaki zai fuskanci shari’a”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel