Nigerian news All categories All tags
EFCC zata fara bincike akan 'yan PDP da aka lissafo sunayen su a jerin sunayen barayin gwamnati

EFCC zata fara bincike akan 'yan PDP da aka lissafo sunayen su a jerin sunayen barayin gwamnati

- An bawa hukumar yaki da masu yiwa arzikin ta'annati (EFCC) umurnin daukar mataki a kan barayin gwamnati

- Hukumar tace tuni ta fara aiki a kan daukar matakin ga wadanda suka sace kudaden gwamnatin

- A baya, gwamnatin ta bayyana jerin sunayen wadan da ake zargi da dibar kudaden gwamnatin

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin ta'annati (EFCC) zata fara bincike akan wadanda sunayensu suka fito a cikin jerin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na wadanda suka saci kudaden gwamnati.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa yawancin wadanda sunayensu suka fito a cikin jerin ‘yan jam’iyyar PDP ne.

EFCC zata fara bincike akan 'yan PDP da aka lissafo sunayen su a jerin sunayen barayin gwamnati

EFCC zata fara bincike akan 'yan PDP da aka lissafo sunayen su a jerin sunayen barayin gwamnati

KU KARANTA: Tazarcen Ganduje: Dalilai hudu da kan iya kai shi ga Nasara

Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta ce "Mun fara tattaro takardun fara bincike a kansu"

Ministan Labarai, Alhaji Lai Mohammed shine ya fitar da jerin sunayen, inda ya bayyana cea “PDP ta kalubalance mu da mu fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati, bayan sun san cewa an karar da asusun gwamnati a lokacin da suke kan mulki. Amma duk da haka suke wannan ikirari”.

Channel TV ta bayyana cewa an fara fitar da jerin sunayen a ranar 1 ga watan Afirilu, inda har wasu mutane ke korafin cewa sunayen sunyi kadan, Ministan labarai da al’adun yace anyi wannan ne a matsayi somin tabi, lokacin da yake bayyana sabon jerin da aka fitar a jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel