Nigerian news All categories All tags
Hukumar kiyaye hadura tayi gargadi akan tuki yayinda mutum ke cikin maye

Hukumar kiyaye hadura tayi gargadi akan tuki yayinda mutum ke cikin maye

- Kwamandan Hukumar kiyaye hadura na kasa na yankin birnin tarayya (CC) Ayuba Agora Wobin, ya gargadi masu tuki yayinda suke cikin maye da su guji tuki bayan sun sha kwaya ko giya

- Ya jadadda bukatar masu baburan haya dasu mallaki takardar shaidar tuki

Hukumar kiyaye hadura tayi gargadi akan tuki yayinda mutum ke cikin maye

Hukumar kiyaye hadura tayi gargadi akan tuki yayinda mutum ke cikin maye

Kwamandan Hukumar kiyaye hadura na kasa na yankin birnin tarayya (CC) Ayuba Agora Wobin, ya gargadi masu tuki yayinda suke cikin maye da su guji tuki bayan sun sha kwaya ko giya.

DUBA WANNAN: Mutane 3 sun kone kurmus yayinda wata mota ta kama da wuta a hanyar Abuja

Wobin yayi Kiran ne yayin da yake jawabi ga matukan baburan na yankin Tungan Maje, Anagada, Dei Dei, Gwagwa da kuma Zuba a ranar Talatar nan. Ya kuma ja kunnen matuka baburan akan kaucewa dokar hanya, cewa yawancin hatsarurrukan da ke faruwa a Zuba masu babura ke haddasasu ta hanyar kaucewa dokokin hanya.

Ya jadadda bukatar masu baburan haya dasu mallaki takardar shaidar tuki, kari da cewa su kasance koyaushe da Hular tuki domin su kare kansu daga munanan raunuka yayin hatsarurruka.

Yace mafi yawan hatsarurrukan da suke ritsawa da babura da sauran abun hawa sakamako ne na halin ko in kula na masu baburan haya. Ta yanda da yawansu suna tuki ne karkashin buguwa da sukayi da barasa da kuma kwayoyi. "Ya zama dole ku mallaki shaidar ku ta tuki da kuma lambar abin hawa koda kuwa saboda sace sace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel