Buhari bai isa ya kashe $1bn wajen siyan makamai ba har sai mun amince da hakan – Sanata Ben Bruce

Buhari bai isa ya kashe $1bn wajen siyan makamai ba har sai mun amince da hakan – Sanata Ben Bruce

- Sanata Ben Bruce yace shugaban kasa Buhari ba zai iya amincewa da kudi don yakar Boko Haram ba

- Yace sai dai kawai ya bayar da shawarwari

- Sanatan na Bayelsa yace majalisar dokoki ce kadai zata iya amincewa da hakan

Sanata Ben Murray Bruce yayi martini ga amincewa das akin dala biliyan 1 da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi domin siyan makaman da zaa yaki yan ta’addan Boko Haram cewa akwai bukatar majalisar dattawa ce zata amince da hakan.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanatan na Bayelsa yayi Magana a ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu cewa shugaba Buhari na bukatar yardarm majalisar dokoki wajen kashe wadanan makudan kudade.

Buhari bai isa ya kashe $1bn wajen siyan makamai ba har sai mun amince da hakan – Sanata Ben Bruce

Buhari bai isa ya kashe $1bn wajen siyan makamai ba har sai mun amince da hakan – Sanata Ben Bruce

Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasa Buhari ya amince das akin dala biliyan daya domin siyan makamai don taimakawa wajen yaki da yan ta’addan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Tambuwal da Wamakko basa adawa da Shugaba Buhari Tambuwal da Wamakko basa adawa da Shugaba Buhari

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu bayan taron tsaro tare da shugaban kasar. Yace sun duba lamarin halin da tsaro ke ciki kafin shugban kasar ya amince da siyan Karin kayayyaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel