Nigerian news All categories All tags
Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Adamu Garba II yace zai doke Buhari a zaben dan takarar jama’iyyar ta APC

- Adamu yace tsayawarsa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ba wai kamfen bane ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Adamu ya bayyana cewa cancantarsa ce zatasa ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta APC

Mai neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Adamu Garba yace, ba gudu ba ja da baya akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta APC.

Yace saboda yafi kowa cancanta a jam’iyyar, inda yace zai doke shugaba Buhari a zaben dan takarar jam’iyyar na wannda zasu bawa tikiti a zaben 2019.

Adamu Garba ya kara da cewa ya zabi zam’iyyar ne saboda yana ganin cewa ita kadai ce jam’iyyar da zata bawa matasa dama. Ya bayyana haka ne a wurin wani taro a jihar Legas, lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

Zan doke Buhari a zaben dan takara na jam’iyyar APC - Garba

Garba yace yana hanyoyi da dama wadanda zaiyi amfani dasu ya maganace matsalolin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Jam’iyya: Gwamna El-Rufai yayi kaca-kaca da manyan Gwamnonin APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an nemi ayi baram-baram a taron da Gwamnonin Jam’iyyar APC su kayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. A wajen taron Shugaban Gwamnonin APC ya bayyana cewa sun goyi bayan a cire John Oyegun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel