Nigerian news All categories All tags
An gurfanar da dan sandan da ya taimakawa masu laifi tserewa daga kurkuku

An gurfanar da dan sandan da ya taimakawa masu laifi tserewa daga kurkuku

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Osun ta gurfanar da wani jami'inta, Saja Ajayi Sunday; mai shekaru 38, gaban kotun majistare dake Osogbo bisa zarginsa da taimakawa wasu masu laifi tserewa daga gidan yari.

An gurfanar da Saja Sunday gaban alkalin kotu majistare, A. O Ajanaku, ranar Litinin bisa tuhumar sa da laifuka guda biyu; sakaci da kuma taimakon masu laifi mutum biyu; Kaseem Oladehinde da Idowu Hassan, dukkansu ana tuhumar su da laifin sata.

Dan sanda mai gabatar da kara, Inspekta Elisha Olusegun, ya shaidawa kotun cewar, jami'in dan sandan da wasu mutum biyu da yanzu haka sun tsere, sun aikata laifin ne ranar 1 ga watan Nuwamba, 2017, da misalin karfe 5:00 na yamma.

An gurfanar da dan sandan da ya taimakawa masu laifi tserewa daga kurkuku

An gurfanar da dan sandan da ya taimakawa masu laifi tserewa daga kurkuku

Ya kara da cewar, laifin jami'in ya saba da sashe 137 na kundin aikata laifuka a jihar Osun kuma an tanadi hukunci a sashe 138 a cikin kundin hukuncin aikata laifuka da jihar ta kirkira a shekarar 2003.

DUBA WANNAN: Farfadiya gare shi, ba mu muka kashe shi ba - Hukumar soji ta musanta kisan farar hula a jihar Taraba

Lauyan dake kare dan sanda Saja Sunday ya nemi kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa tunda ba a tabbatar ya aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Mai shari'a Ajanaku ya amince da bukatar lauyan tare da bayan da beli a kan kudi N500,000 da kuma shaidu guda biyu da su ma zasu ajiye adadin kudin kuma tilas daya daga cikinsu ya kasance ma'aikacin gwamnatin tarayya da ya mallaki wata kadara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel