Jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe

Jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe

- Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe da majalisa Najeriya tayi

- Gamawa ya ce Najeriya ta shiga halin kaka na kayi a karkashin gwamnatin jam'iyyar APC, sannan kuma jam'iyyar APC ita ce ummul aba'isin kawo talauci, yunwa, cututtuka da kuma tsadar rayuwa ga al'umma

Jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe

Jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe

Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe da majalisa Najeriya tayi. Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Babayo Garba Gamawa, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake magana da manema labarai a jihar Bauchi.

DUBA WANNAN: Buhari ya bada izinin sayo makamai na kimanin Dala Biliyan Daya

Ya ce, jam'iyyar PDP jam'iyya ce dake bin doka, don haka tana maraba da tsarin da majalisar ta bayar na sake salon zaben, saboda a yanzu haka sune suke da mafi yawan mabiya a kasa nan.

Gamawa ya ce Najeriya ta shiga halin kaka na kayi a karkashin gwamnatin jam'iyyar APC, sannan kuma jam'iyyar APC ita ce ummul aba'isin kawo talauci, yunwa, cututtuka da kuma tsadar rayuwa ga al'umma. Inda ya kara da cewa rayuwar talaka tafi inganci a lokacin da jam'iyyar PDP ke kan mulki, sannan ya bayyana cewar jam'iyyar APC ta kasa cika alkawuran da ta daukar wa 'yan Najeriya a lokacin kamfen din shekarar 2015.

Ya ce, jam'iyyar PDP zata sake dawowa mulki domin ganin ta sake inganta rayuwar al'umma ta hanyar aiwatar da ayyukan cigaba ga al'umma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel