Nigerian news All categories All tags
Gwamnonin APC 2 na neman kiran taron shugabannin jam'iyya da ya sabawa ka'ida

Gwamnonin APC 2 na neman kiran taron shugabannin jam'iyya da ya sabawa ka'ida

A wani yunkuri da ka iya haifar da rikici a jam'iyya mai ci ta APC (All Progressive Congress), wasu gwamnoni biyu na dandalin jam'iyyar sun kammala shirye-shiryen su na hada taron shugabannin jam'iyyar da ya sabawa ka'idoji da kuma dokokin ta.

Jaridar Leadership ta fahimci cewa, wannan gwamnonin biyu ma su shirin aikata katsalandan sun fito ne daga yankunan Arewa da kuma Kudancin kasar nan, inda suke yunkurin sauya ka'idoji jam'iyyar na hada taron da ya sabawa duk mataman ta tun daga kananan hukumomi zuwa ga na kasa baki daya.

Shugaban jam'iyyar APC; Cif John Odigie-Oyegun

Shugaban jam'iyyar APC; Cif John Odigie-Oyegun

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, kundin tsari na jam'iyyar APC ya bayar da dama ta sanar da gayyato taron shugabannin jam'iyya kafin makonnin biyu, inda kundin tsarin ya kuma bayar da dama ta bayar da sanarwa kafin kwanaki bakwai matukar taron ya kasance na gaggawa.

Sai dai wata majiya mai karfi ta shaidawa manema labarai cewa, gwamnonin sun yi murdiya a cikin kwanan wata da suka sanya a wasiƙar su ta gayyato taron da zai bayar da rata ta kwanaki bakwai kafi gudanar da shi kamar yadda doka ta tsara.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta damko fiye da muggan makamai 70 a garin Kaduna

Majiyar ta kuma yi gargadin cewa wannan taro na shugabannin jam'iyyar zai iya kara harzuka rikici a tsakanin gwamnonin jam'iyyar a yayin da suke da dama ta daukaka kara har gaban Kuliya domin ta tsawatar.

Wata majiya mai karfi ta kuma shaidawa manema labarai cewa, gwamnonin biyun da suka nuna rashin goyon bayan su kan jagorancin John Odigie-Oyegun, sun kuma bayyana ra'ayin su na cewar kafa kwamitin kula da jam'iyyar shima ya sabawa doka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel