Nigerian news All categories All tags
Rikicin Jam’iyya: Gwamna El-Rufai yayi kaca-kaca da manyan Gwamnonin APC

Rikicin Jam’iyya: Gwamna El-Rufai yayi kaca-kaca da manyan Gwamnonin APC

Daily Trust ta rahoto cewa an nemi ayi baram-baram a taron da Gwamnonin Jam’iyyar APC su kayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. A wajen taron Shugaban Gwamnonin APC ya bayyana cewa sun goyi bayan a cire John Oyegun.

Shi ma dai Shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulaziz Yari yayi jawabi bayan Rochas Okorocha inda yace sun yi na’am da matakin da Shugaban kasa Buhari ya dauka na cewa Jam’iyyar ta gudanar da sabon zabe kamar yadda ya dace.

Rikicin Jam’iyya: Gwamna El-Rufai yayi kaca-kaca da manyan Gwamnonin APC

Shugaban Gwamnonin Arewa Shettima bai ce komai ba a taron APC

Labari ya zo mana cewa Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i yayi wuf ya maidawa manyan Gwamnonin martani inda yace a daina ci masu tuwo a kwarya don ba su yi mubaya’a game da cire Shugaban Jam’iyya John Oyegun ba.

KU KARANTA:

El-Rufai yake cewa duk Gwamnonin APC babu wanda ya san Shugaba Buhari irin sa, kuma jawabin da Buhari yayi kwanaki ba ya nufin a tsige Oyegun sai dai kurum yana nufin ayi shawara. Shugaba Buhari dai yace ya gano bai kamata Oyegun ya zarce ba.

Bayan nan wasu Gwamnonin Jam’iyyar irin su Abdullahi Ganduje da kuma masu goyon bayan Oyegun ya zarce sun sa baki inda su ka nemi su halatta tazarcen Shugaban na APC. Farfesa Osinbajo wanda rikakken Lauya ne dai yace ba haka abin yake ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel