Gwamnonin APC da su ka shiga-su ka fita domin a karawa Oyegun wa’adi

Gwamnonin APC da su ka shiga-su ka fita domin a karawa Oyegun wa’adi

- Wasu Gwamnonin APC su na tare da Shugaban Jam’iyyar APC

- Irin su Gwamna El-Rufa’i ne su ka sa aka kara wa’adin Oyegun

- Sai dai mafi yawan Gwamnonin na APC sun nemi ayi sabon zabe

Mun samu labari daga Daily Trust cewa akwai wasu masu goyon bayan John Odigie-Oyegun ya zarce a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa wanda ta sa Shugaban kasa ya nuna cewa ba ya tare da su a wannan magana gudun kar a shiga Kotu.

Gwamnonin APC da su ka shiga-su ka fita domin a karawa Oyegun wa’adi

Bagudu, Ambode da Ajimobi sun nemi a cire Oyegun

Gwamnoni dai 15 na APC su ka sa hannu a makon nan cewa a gudanar da sabon zabe na Shugabannin Jam’iyya. Gwamnonin sun hada da Abdul-Aziz Yari, Abdullahi Ganduje, Kashim Shettima, Aminu Tambuwal da wasu Gwamnonin kasar.

KU KARANTA: Abubuwan da za su hana Shehu Sani komawa Majalisa

Sai dai Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai da kuma Simon Lalong da Yahaya Bello da Rotimi Akeredolu ba su tare da sauran Gwamnonin inda su kayi kutun-kutun kwanaki aka kara wa’adin Shugabannin Jam’iyyar da shekara guda.

Ana kuma tunani Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar zai goyi bayan wadannan Gwamnoni 4. Sai dai zai yi wahala Oyegun din ya cigaba da zama a kujerar sa saboda mafi yawan Gwamnonin Jam’iyyar ba su yi na’am da hakan ba yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel