Buhari ya bada izinin sayo makamai na kimanin Dala Biliyan Daya

Buhari ya bada izinin sayo makamai na kimanin Dala Biliyan Daya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gwamnatin tarayya ta bada naira miliyan 360 domin sayen kayan aiki ga jami'an tsaro don yaki da masu tada kayar baya da kuma karfafa tsaro a kasar nan

Buhari ya bada izinin sayo makamai na kimanin Dala Biliyan Daya

Buhari ya bada izinin sayo makamai na kimanin Dala Biliyan Daya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gwamnatin tarayya ta bada naira miliyan 360 domin sayen kayan aiki ga jami'an tsaro don yaki da masu tada kayar baya da kuma karfafa tsaro a kasar nan.

Ministan tsaro na kasa Mansur Dan Ali, shine ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai a ranar Larabar nan data gabata, jim kadan bayan fitowar shi daga wata ganawa da suka yi da Shugaban kasar tare da Shugabannin hukumomin tsaro.

DUBA WANNAN: Mace ta kori zaki da kara don kar ya cinye mata akuyarta

"Abinda zan ce shine, ina so na sanar daku cewar, kwanan nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada izinin sayen makamai ga ma'aikatan mu na hukumar tsaro, wanda kudin su ya kai kimanin dala biliyan 1," inji ministan.

A wani taro da aka yi akan tattalin arziki shekarar data gabata, inda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta, tare da dukkanin gwamnonin jihohi, an yanke shawarar za ayi ciri dala biliyan daya daga asusun rarar kudin danyen mai domin karfafa tsaro a kasar nan.

Ministan tsaro yace taron da aka gabatar a jiya, an tattauna ne akan rashin tsaro da yake damun jihohin kasar nan musamman ma irin su Taraba, Zamfara, Benue da dai sauran su. Ya ce gwamnati ta na kokari wurin tabbatar da tsaro musamman ma a wuraren da rashin tsaron yayi wuya.

"Hakika mun kara karfin ma'aikatan mu na tsaro, ciki kuwa harda rundunar tsaro ta sojan sama. Sannan ya bayyana cewar gwamnati tana kokari wurin ganin an samo hanyar da za abi domin ganin an ceto yarinyar data rage a hannun 'yan Boko Haram.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel