Nigerian news All categories All tags
Mun samu ayyuka sama da 100 da Gwamnatocin baya su ka gaza karasawa - Gwamnatin Buhari

Mun samu ayyuka sama da 100 da Gwamnatocin baya su ka gaza karasawa - Gwamnatin Buhari

- Gwamnatin Buhari ta maida martani ga masu cewa ta gaza yin ayyuka

- Wani Hadimin Buhari yace kammala ayyukan baya ake yi ba sababbi ba

- Gwamnatocin baya dai sun dauko ayyuka da dama da su ka gaza a Kasar

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana abin da ya hana ta dauko wasu sababbin kwangiloli a Kasar nan bayan jama'a sun nuna cewa babu wani aiki da Gwamnatin nan ta faro ta iya gamawa har yau.

Mun samu ayyuka sama da 100 da Gwamnatocin baya su ka gaza karasawa - Gwamnatin Buhari

Gwamnatin Buhari ta tunkarin aikin Enugu zuwa Onicha

Wani Hadimin Shugaban kasa Buhari Tolu Ogunlesi ya bayyana cewa sun ci gadon manyan ayyuka kusan 120 a Kasar don haka babu dalilin kara kinkimo wasu sababbin ayyuka domin kurum ace Gwamnatin Bubari ita ma tayi aiki.

KU KARANTA: Abubuwa 3 da za su hana Shehu Sani komawa kujerar Sanata a 2019

Ogunlesi ya nuna cewa kammala aiki ba abu bane mai sauki shiyasa Shugabannin baya su ka gaza kammala ayyukan da su ka fara. Hadimin Shugaban kasar yace yanzu haka an kammala aikin jawo lantarki daga iska a Jihar Katsina.

Bayan wannan ma akwai hanyoyin da wannan Gwamnati ta gada da ta ke ta aiki. Daga ciki akwai hanyar Enugu zuwa Onitsha wanda jama'a ke ta murna ganin yadda ake ta aiki a gadan-gadan. A baya dai an yi sake da wannan ayyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel