Rikicin jam’iyyar APC: Gwamnoni sun yi ma Oyegun tsutsu, amma zai dawo ta bayan gida

Rikicin jam’iyyar APC: Gwamnoni sun yi ma Oyegun tsutsu, amma zai dawo ta bayan gida

Gwamnonin jam’iyyar APC sun tabbatar da karewar wa’adin mulkin shugaban jam’iyyar, John Odigie-Oyegun, tare da sauran shuwagabannin jam’iyyar tun daga sama har kasa, inji rahoton Daily Trust.

Gwamnonin sun yanke wannan mataki ne a yayin wata ganawa da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadr gwamnatin tarayya dake Abuja, a ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Masarautar Daura ta tafka babbar asara da mutuwar Sanata Mustapha Bukar –Mai martaba Sarkin Daura

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnonin sun bayyana cewar Oyegun tare da sauran shuwagabannin jam’iyyar na da damar sake tsayawa takara don cigaba da mike kafa a kan mukaman da suke danawa.

Rikicin jam’iyyar APC: Gwamnoni sun yi ma Oyegun tsutsu, amma zai dawo ta bayan gida

Buhari da Oyegun

Shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Anayo Rochas Okorocha ba jihar Imo ne ya sanar da haka ga manema labaru, inda yace: “Bari in yi karin haske game da babban taron jam’iyyarmu da zaben shuwagabannin da za’a yi, hakan ba yana nufin shuwagabannin jam’iyyar sun gaza bane.

“Kuma zasu iya dawowa ta hanyar tsayawa takara, abinda muke cewa kawai shi ne zangon mulkinsu yazo karshe, amma duk masu son cigaba da dafe mukamansu, zasu iya sake tsayawa takara, don haka wannan ba wani abin rikici bane a tsakanin yayan jam’iyyarmu, tsinya muke, madaurinki guda” Inji shi.

Daga karshe Rochas ya bayyana cewar a yayin ganawarsu da shugaban kasa Muhammadu Buhar, sun tattauna yadda za’a shirya zabukan shwuagabannin jam’iyyar, inda yace nan bada dadewa ba za’a sanar da kwamitin zaben tare da ranar zaben.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel