Nigerian news All categories All tags
Wani Matashi ya gurfana gaban Kuliya da laifin fyade diyar makwabci a jihar Legas

Wani Matashi ya gurfana gaban Kuliya da laifin fyade diyar makwabci a jihar Legas

A ranar Larabar da ta gabata ne wata kotun majistire dake zamanta a unguwar Ebute Meta ta jihar Legas, ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 24, Jami'u Hussaini, a bisa aikata laifi na fyade diyar makwabcin sa 'yar shekaru 14 da haihuwa.

Hussani wanda mazaunin gida mai lamba 102 a kan titin Bornu na unguwar Ebute Meta ta jihar ya gurfana gaban Kuliya da laifin fyade, sai kawowa yanzu Kotun ba ta kama shi da laifin da ake tuhumar sa ba.

Mista Chinalu Uwadione, Jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa Kotun cewa, Hussaini dai ya aikata wannan laifin ne da misalin karfe 11.00 na daren ranar 27 ga watan Maris, inda ya yiwa matashiyar ta karfi wajen debe kwazabar sa ta da namiji.

Wani Matashi ya gurfana gaban Kuliya da laifin fyade diyar makwabci a jihar Legas

Wani Matashi ya gurfana gaban Kuliya da laifin fyade diyar makwabci a jihar Legas

Jami'i Chinalu ya ci gaba da cewa, wannan laifi ya sabawa dokar miyagun laifuka ta jihar Legas sashe na 137 wanda babu hukunci face na kisa ga duk wanda ya aikata makamancin sa.

KARANTA KUMA: Ababe 3 dake haddasa cutar Sankarau a Najeriya

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, alkaliya a Kotun Misis A. Ipaye-Nwachukwu, ta daga sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Mayu, inda kuma ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Hussaini ba tare da bayar da beli ba.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng a ranar da ta gabata ta ruwaito cewa, akwai wasu jerin jihohi 16 da suka sha fama da cutar Sankarau a 'yan lokuta kadan da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel