Nigerian news All categories All tags
Da duminsa: Jami'an tsaron Najeriya sun sace wani dan majalisar jiha

Da duminsa: Jami'an tsaron Najeriya sun sace wani dan majalisar jiha

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa kawo yanzu dai jami'an tsaron Najeriya ana kyautata zaton sune suka sace dan majalisar jihar Ekiti kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar mai suna Honarable Gboyega Aribisogan.

Kamar dai yadda muka samu, an cewa da sanyin safiyar yau ne dai aka ce jami'an tsaron sun yi awon gaba dan majalisar inda kuma ake kyautata zaton sun tafi da shi a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Da duminsa: Jami'an tsaron Najeriya sun sace wani dan majalisar jiha

Da duminsa: Jami'an tsaron Najeriya sun sace wani dan majalisar jiha

KU KARANTA: Shin kuna da labarin tsohuwar matar Dangote?

Da yake karin haske game da lamarin, kanin dan majalisar mai suna Sola ne ya bayyana cewa wata tawagar jami'an 'yan sandan nan ta musamman dake hana manyan laifukan fashi da makami na musamman watau Special Anti Robbery Squad (SARS) da kuma 'yan sandan farin kaya ne suka tafi da shi.

A wani labarin kuma, Yayin da shirye-shire ke ta dada kara kankama game da zabukan kananan hukumomin jihar Nasarawa dake a shiyyar Arewa ta tsakiya a wata mai kamawa, da alamu kawunan masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC mai mulki a jihar sun rabu.

Mun samu dai cewa jiga-jigan jam'iyyar ta APC a jihar dai tuni suka kai kukan su gaban gwamnan jihar inda suka roke shi da ya duba girman Allah kar ya kakaba masu shugabannin da ba su so a kananan hukumomin na su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel