Nigerian news All categories All tags
Gwamnati na son bin diddigin inda Boko Haram da masu laifuka ke samo kudi, dubi ta inda ta faro

Gwamnati na son bin diddigin inda Boko Haram da masu laifuka ke samo kudi, dubi ta inda ta faro

- An dade ana mamakin yadda cikin dare daya aka sami watsuwar makamai da kudaden aikata manyan laifuka a kasar nan

- Gwamnati ta ce zata bi diddigin lamarin don samun mafita

- A karshe kuma, zata toshe dukkan hanyoyi da ke taimakawa ta'addanci samun kudade

Gwamnati na son bin diddigin inda Boko Haram Haram da masu laifuka ke samo kudi, dubi ta inda ta faro

Gwamnati na son bin diddigin inda Boko Haram Haram da masu laifuka ke samo kudi, dubi ta inda ta faro

Daukar nauyin yan'ta'adda: gwanatin tarayya ta fara yunkurin kwace rijistar kungiyoyin taimakon kai da kai marasa tushe:

Gwanatin tarayya ta fara kammala kungiyoyin taimakon kai da kai kimanin guda dari wadanda suka kaucewa manufarsu.

Daraktan cibiyar sanya-ido ta kudi ta Najeriya, Mista Francis Usani yace a Abuja Ranar Laraba "Kammala kungiyoyin da basu da amfani ya zama dole idan akayi la'akari da cewa dasu ake amfani don daukar nauyin almundahana ta kudi da kuma ta'addanci a Najeriya da kuma sauran kasashen yammacin Afirika.

Usani yayi wannan zancen ne a bude bikin kungiyoyin gwanatin masu kare almundahana ta kudi a yammacin Afirika wadda akafi sani da GIABA. A taron horarwa da tayi na kwana uku akan ingantattun hanyoyin gyara tareda fada da almundahana da tallafawa ta'addanci ta karkashin kungiyoyi marasa amfani.

DUBA WANNAN: Yau shekaru biyar da yafiya ga Boko Haram

Taron wanda aka fara ranar laraba za'a karasa shi ranar juma'a ne. GIABA sun fito da sabon salon makala haraji ga kasashen goma sha takwas wadanda ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen Afirika ta yamma domin magance almundahana ta kudi da tallafawa ta'addanci.

Usani yayi bayanin yanda za'a kammala da kuma tace kungiyoyin ba don murkushe kungiyoyin taimakon ba sai domin magance tallafawa ta'addanci. Ya tabbatar da cewa duk kungiyar da bata tsallake gwajin da za'ayi mata ba za'a kwace rijistar ta. Zamu cigaba da tantancewar har sai mun gano kungiyoyin da suke abin da ya dace da wadanda suke akasin hakan

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel