Nigerian news All categories All tags
Osinbajo naso kowanne dan Najeriya ya sami inshorar asibili kan lafiya

Osinbajo naso kowanne dan Najeriya ya sami inshorar asibili kan lafiya

- Miliyoyin 'yan Najeriya basu da inshorar lafiya

- Inshorar laiya kamar asusu ne da kowa zai sanya kudinsa kadan domin kula da lafiyarsa a shekara

- Osinbajo na so kowa ya samu

Osinbajo naso kowanne dan Najeriya ya sami inshorar asibili kan lafiya

Osinbajo naso kowanne dan Najeriya ya sami inshorar asibili kan lafiya

Osinbajo ya karfafa tilasta inshorar kiwon lafiya ga yan' Najeriya: Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya karfafa dacewar tilascin inshorar kiwon lafiya ga yan' kasar domin su samu ingantattu da saukakken kayayyakin kiwon lafiya.

Yayi jawabin ne a yau laraba a Abuja a "Dakin kirkire kirkire : launch pad for social innovators". Mista Osinbajo ya jadada cewa cibiyar inshorar lafiya ta kasa duk da amfanin ta amma ta kasa tattara ingantattu abubuwan bukata domin tallafi ga lafiyar jama'a.

Yace gwamnati tana kudade a bangaren ilimi da kuma lafiya kuma ta tallafawa jihohi da tiriliyan N1.91. Ya kara da cewa abu daya da kasar ya dace ta riqe, shine nagarta. Domin kuwa da nagarta ne kashi hamsin na matsalolin kasar zasu kai.

DUBA WANNAN: MAce ta kori zaki saboda ceton akuyarta

Kamar yanda ya fada, kasar na da albarkatu da dama da kuma kirkire kirkire wanda zai amfani kasar da shugabanci me nagarta.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa mutane suna shiga siyasar kasar ne Don su yi arziki ta hanyar sata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel