Harin baya-bayan nan na Zamfara: 54 ne suka mutu, 7,000 suka rasa muhallansu

Harin baya-bayan nan na Zamfara: 54 ne suka mutu, 7,000 suka rasa muhallansu

- Jihar Zamfara dai ta zama kamar Sambisa

- Ana kaiwa jama'a hari a kauyuka ba kuma abinda suka yi

- LAmarin ya sanya an tura sojojin kwantar da barazana yankin

Harin baya-bayan nan na Zamfara: 54 ne suka mutu, 7,000 suka rasa muhallansu

Harin baya-bayan nan na Zamfara: 54 ne suka mutu, 7,000 suka rasa muhallansu

Matsalar tsaro a yankin Arewa maso yamma, a jihar Zamfara ya dauki sabon salo, inda kawai sai mayaka su fito daga hamada su fara kashe mutane su kone musu muhallansu su kuma tsere daji, bayan haka kuma sai su koma kan wani kauyen in an kwan biyu.

Har yanzu dai babu takamai-mai ko wata kungiya ce ke irin wannan aika-aika da sunan siyasa, kudi ko addini. Sai dai jihar tana aiki da shari'ar Islama ne tun daga 2000 bayan da gwamna Yarima Sani ya ayyana ta a fadin jihar.

DUBA WANNAN: Shekaru biyar kenan da GEJ yayi afuwa ga Boko Haram

A yanzu dai gwamnatin tarayya ta tura sojoji domin murkushe barazanar, kuma a watan jiya shugaba Buhari ya ziyarci yankin don gane wa idanunsa me ke abkuwa.

A kowanne hari ana asarar rayuka da dama. A wannan na baya-baya shugaban hukumar Nema dake kula da 'yan gudun hijira a yankin yace akalla mutum 54 ne aka kashe, kuma 7,000 sun tsero da iyalansu domin samun mafaka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel