Nigerian news All categories All tags
Sharhi kan Siyasar APC a 2019: Buhari ya gwammace abota da Tinubu kan Oyegun, Gwamnoni sun zabi biyayya ga Buhari suma

Sharhi kan Siyasar APC a 2019: Buhari ya gwammace abota da Tinubu kan Oyegun, Gwamnoni sun zabi biyayya ga Buhari suma

- Shi dai Tinubu ya dawo daga rakiyar Oyegun kuma ya shaidawa Buhari

- Buharin ya san amfanin da Tinubu zaiyi, ko kuma barnar da zayyi muddin ba'a faranta masa ba

- Gwamnoni ma dai sunbi, bayan da suka ga hanyar laluma da oga yabi

Siyasar APC 2019: Buhari ya gwammace abota da Tinubu kan Oyegun, Gwamnoni sun zabi biyayya ga Buhari suma

Siyasar APC 2019: Buhari ya gwammace abota da Tinubu kan Oyegun, Gwamnoni sun zabi biyayya ga Buhari suma

Gwamnonin APC sun yanke hukuncin goyama shugaba Muhammadu Buhari akan tsawaita lokacin mulkin shuwagabannin jam'iyyar. Hukuncin ya biyo bayan zama na biyu tsakanin Mista Buhari da gwamnonin a ofishinshi ranar laraba.

A ranar talata ne shugaban ya zauna da gwamnonin domin yanke hukuncin hana tsawaita lokacin shugabancin na shuwagabannin ta na kasa da kuma jihohi. A satin da ya gabata ne, Mista Buhari ya sanar da taron da kwamitin zababbun shuwagabannin jam'iyyar ta APC tayi domin shawarta tsawaita shugabancin jam'iyyar na shekara daya wanda ya sabawa kundun tsarin mulki na jam'iyyar APC da kuma najeriya.

DUBA WANNAN: Shekaru biyar kenan da shugaba Jonathan yayi wa Boko Haram Afuwa

An tashi taron ranar talatan ne a inda wasu daga cikin gwamnonin suke goyon bayan haka, wasu kuma na sukar hakan. A daren talatan ne gwamnonin suka hadu su kadai inda suka rankayo zuwa gidan gwanatin tarayya don ganawa da shugaban kasar.

Gwamnonin sun gwammace su yar da Oyegun din su kama dahir, watau Tinubu, ganin shi ke da hanyar ciyo yankinsa a 2019, lissafi da shima Buharin yayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel