Almundahana da kudin kasa a mulkin PDP: Gwamnatin tarayya ta umarci EFCC​ ta gurfanar da mutanen da aka saki sunayensu

Almundahana da kudin kasa a mulkin PDP: Gwamnatin tarayya ta umarci EFCC​ ta gurfanar da mutanen da aka saki sunayensu

Kwanannan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) zata gurfanar da duk wanda sunansa ke cikin jerin mutanen da suka yiwa dukiyar kasa wasoso lokacin mulkin PDP, kamar yadda gwamnatin tarayya ta fitar.

Wani jami'in hukumar EFCC ya tabbatar wa da jaridar The Cable cewar gwamnatin tarayya ta bawa hukumar umarnin gurfanar da duk wanda sunansa ke cikin jerin sunayen da gwamnati ta fitar a karshen makon jiya.

"Muna tattara dukkan takardun da muke da bukata a yanzu haka," a cewar jami'in, ba tare da ya kara wani bayani ba.

Almundahana da kudin kasa a mulkin PDP: Gwamnatin tarayya ta umarci EFCC​ ta gurfanar da mutanen da aka saki sunayensu

Almundahana da kudin kasa a mulkin PDP: Gwamnatin tarayya ta umarci EFCC​ ta gurfanar da mutanen da aka saki sunayensu

Da yawan wadanda suka rike mukami a lokacin mulkin PDP na tsawon shekaru 16 na fuskantar tuhumar cin hanci, saidai ba dukkansu ne aka gurfanar gaban kotu ba.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen wadanda suka wawure dukiyar kasa lokacin mulkin PDP

Daga ciki jerin sunayen da gwamnatin tarayya ta saki akwai tsofin gwamnoni, Sanatoci, da wasu ma da ba 'yan siyasa ba.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya saki sunayen a karo na farko, ranar Juma'a, 30 ga watan Maris, kafin daga bisani ya sake sakin wasu jerin sunayen a karo na biyu, ranar litinin, 2 ga watan Afrilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel