Nigerian news All categories All tags
An tisa keyar wani mutum zuwa gidan yari saboda ya saci ganyen kabewa

An tisa keyar wani mutum zuwa gidan yari saboda ya saci ganyen kabewa

A yau, Laraba, wata kotun majistare dake zamanta a Iyaganku dake garin Ibadan, jihar Oyo, ta yankewa wani mutum, Sunday Peter, mai shekaru 40, hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata guda saboda ya saci kullin ganyen kabewa guda biyar.

Alkaliyar kotun, Abdulateef Adebisi, ta yanke hukuncin ne bayan wanda ake zargi ya amsa laifinsa.

Kazalika, alkalin kotun, ta bashi zabin biyan tarar N5,000 tare da umarnin mayar da ganyen ga mai su na asali.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, Saja Salewa Ahmed, ya shaidawa kotun cewar, wanda ake zargin tare da wani mutum sun aikata laifin ne ranar 1 ga watan Afrilu, a unguwar Ajibode dake garin Ibadan.

An tisa keyar wani mutum zuwa gidan yari saboda ya saci ganyen kabewa

An tisa keyar wani mutum zuwa gidan yari saboda ya saci ganyen kabewa

An gurfanar da Peter bisa tuhumar sa da satar ganyen kabewa da kudinsu ya kai N20,000 a gidan wata mutum, Muideen Adewale.

DUBA WANNAN: Uwa ta kashe diyar ta saboda tana tara samari

"Wanda ake zargin ya shiga gonar Adewale da misalin karfe 6:30 na safe tare da yankar daurin ganyen kabewa mai yawa," inji Saja Ahmed.

Ahmed ya kara da cewar, laifin Peter ya saba da sashe 390(9) na kundin aika laifuka a jihar Oyo, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel