Yau shekara 5 kenan da shugaba Jonathan yayi afuwa ga BH domin su daina fada

Yau shekara 5 kenan da shugaba Jonathan yayi afuwa ga BH domin su daina fada

- A mulkin Yaraduwa ne aka fara yakin Boko Haram

- A mulkin Jonathan abin yayi kamari

- A mulkin Obasanjo suka fara wa'azin ahlussuna da da'awa kafin jihadi

Yau shekara 5 kenan da shugaba Jonathan yayi afuwa ga BH domin su daina fada.

Yau shekara 5 kenan da shugaba Jonathan yayi afuwa ga BH domin su daina fada.

Yau shekaru biyar kenan cur da shugaba Jonathan ya ayyana yafiya ga kungiyar Jama'atu Ahlussunah, Lid da'awati wal jihad.

A 2013 ne dai, bayan da aka ga alamar miyagun da gaske suke, suna ta fatattakar sojoji suna kuma saka bama-bamai a fadin kasar nan, jama'a suka ara kira da suma a gwada yi musu yafiya kamar yadda aka yi wa na Neja Delta.

A lokacin an zaci abin nasu qarau ne, ashe su daula suka tashi kafawa. Sai suka ma fito suka ce su yafiyar Allah kawai suke so ba ta mutum mutum ba, sun zaci wata aljanna zasu je da zarar sun mutu.

DUBA WANNAN: Yadda Abacha ya mutu

Kwatsam, sai gashi kuma wai yanzu ma ana sulhu dasu, karkashin gwamnatin APC, kuma shugaba Buhari ke jagorantar sulhun.

A baya dai kafin su fara samun nasara a filin daga, sun nada shugaba Buhari, lokacin tsohon dan takarar CPC domn ya zama uba gare su, yayi sulhu da gwamnati a madadinsu, ganin cewa da yana kare su kafin ya fahimci inda suka dosa, amma janar din yabi shawarar makiyaya ya janye, yace ba zai tsaya wa kungiyar domin sulhu ba.

Ko yanzu abin zayyi armashi a sabon kokari na sulhun?

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel