Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bada umarnin fitar da kudi naira biliyan 360 don siyan makamai

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bada umarnin fitar da kudi naira biliyan 360 don siyan makamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin fitar da kudi dala biliyan daya, kwatankwacin naira biliyan 360 kenan don siyan makamai ga hukumomin tsaron Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

Ministan harkokin tsaro, Masur Dan Ali ne ya sanar da haka a yayin wata ganawa da yayi da manema labaru a fadar shugaban kasa a ranar Laraba 4 ga watan Afrilu, bayan fitowa daga wata ganawar sirri ta awa uku da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da shuwagabannin hafsoshin Sojin kasar, da sauran shuwagabannin hukumomin tsaro.

KU KARANTA: Halin mutum jarinsa: Dalilai 3 da zasu baiwa El-Rufai nasara a burinsa na Tazarce a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dan Ali yana cewa: “Abinda zan iya fada muku shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci a kashe dalan Amurka biliyan daya don siyan ma Sojojin Najeriya makamai da nufin kawo karshen yaki da ta’addanci".

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bada umarnin fitar da kudi naira biliyan 360 don siyan makamai

Buhari da shuwagabannin hafsoshin tsaro

Dama dai a shekarar data gabata ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo tare da gwamnonin Najeriya suka amince a ware dalan Amurka biliyan guda daga asusun rarar man fetur don siyan makaman yaki da barazanar tsaro.

Bugu da kari, Ministan ya bayyana cewar a yayin ganawarsu da shugaban kasa, sun tattauna batutuwanda suka shafi matsalolin tsaro a jihohin Taraba da Zamfara, inda yace gwamnati zata kafa sabbin rundunonin Soji a jihar Katsina, Sakkwato da Zamfara don magance matsalar.

Daga karshe yace gwamnati na iya bakin kokarinta ta hanyar amfani da duk wasu hanyoyin da take da su don ganin an ceto rayuwa dalibar nan daya tilo yar makarantar Dapchi da ta rage a hannun yan Boko Haram, Leah Sharibu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel