Nigerian news All categories All tags
Dalilin da za su jawo Sanata Shehu ya gaza komawa Majalisar Dattawa

Dalilin da za su jawo Sanata Shehu ya gaza komawa Majalisar Dattawa

Mun kawo maku wasu dalilan da za su sa Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Kwamred Shehu Sani wanda ya ke rikici da Gwamnan Jihar sa Nasir El-Rufai ya gaza komawa kujerar sa a zaben 2019.

Daga cikin wadanda za su kawowa Fitaccen ‘Dan Majalisar cika akwai:

Dalilin da za su jawo Sanata Shehu ya gaza komawa Majalisar Dattawa

Ana iya hana Sanata Shehu komawa Majalisar Dattawa

1. Gwamna Nasir El-Rufai

Tun bayan hawan Gwamna Nasir El-Rufai ya fara samun matsala da Sanatan na sa. Yanzu haka akwai kishin-kishin din cewa wani mai ba Gwamnan shawara zai maye gurbin Shehu Sani a Majalisar Dattawa a 2019.

KU KARANTA: Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Gwamnatin Buhari

2. Jam’iyyar APC

Shehu Sani ya samu matsala da Jam’iyyar sa ta APC mai mulki wanda har ta kai aka dakatar da shi kuma ya shiga ‘Yan taware. Zai yi wahala Jam’iyyar ta ba Sanatan tikiti a zabe mai zuwa saboda wannan rigimar.

3. Mazabar sa

Sanata Shehu Sani bai da magoya baya sosai a Mazabar sa inda kuma wasu su ke jin cewa sun yi da-na-sanin zaben Sanatan wanda kullum ya ke sukar Gwamnatin Shugaba Buhari yana kuma kara yi wa Jam’iyya adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel