Nigerian news All categories All tags
Yan Majalisa 5 da suka rasu lokacin da suke kan mulki

Yan Majalisa 5 da suka rasu lokacin da suke kan mulki

Kamar yadda muka sani mutuwa riga ce wacce sanya ta ya zamo wajibi ga duk wani mai rai a doron kasa. Sannan kuma majalisar wakilan Najeriya kunshe take da wakilai daga mazabu daban-daban na jihohin kasar.

Wasu yan majalisa kan hadu da ajalinsu ne a yayinda suke kan mulki, hakan ne ya sa muka yi duba ga baya wato waiwaye domin tunawa da wasu daga cikin wakilan da suka rasu a yayinya sukewa jihohinsu da al'ummansu bauta.

Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara a ranar Laraba yayi jimamin rasuwa daya daga cikin ‘yan majalissar, mai wakiltar jihar Katsina Bello Sani.

Kafin rasuwar Sani ya kasance mai wakiltar mazabar Mashi/Dutsi, daga jam’iyyar APC, ya mutu yanada shekaru 51.

Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyara jihar Bauchi, domin yin gaisuwa bisa ga rasuwar dan majalisa Ali Wakili, wanda ke wakiltar Bauchi ta kudu dan jam’iyyar APC, ya rasu a gidansa dake birnin tarayya a ranar 17 ga watan Maris, ya rasu yana da shekaru 58.

Yan Majalisa 5 da suka rasu lokacin da suke kan mulki

Yan Majalisa 5 da suka rasu lokacin da suke kan mulki

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya nuna damuwarsa bisa ga rasuwar Hon. Umar Buba Jibril, dan jam’iyyar APC, wanda ke wakiltar Lokoja a jihar Kogi kafin rasuwarsa, kuma shine mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar, ya mutu yana da shekaru 57.

KU KARANTA KUMA: Hukumar ‘Yan Sanda sun rusa kamfanin da ake hada bindigogi a jihar Ebonyi

Mustapha Bukar dan majalissa ne mai wakiltar Katsina ta Arewa, kuma dan jam’iyyar APC, ya kasance yana wakiltar mazabar shugaban kasa, sannan shine shugaban masu rinjaye a majalissar, ya rasu yana da shekaru 63.

Isiaka Adeleke mai wakiltar jihar Osun ya mutu, kafin mutuwarsa ya kasance ciyaman na kwamitin majalissa na fannin harkokin kasuwanci, kuma dan Jam’iyyar APC, Adeleke yam utu yana da shekaru 62.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel