Nigerian news All categories All tags
Lawan yayi jinjina ga kwamitin wayar da kan jama’a na majalisar zartarwa

Lawan yayi jinjina ga kwamitin wayar da kan jama’a na majalisar zartarwa

- An ba jigon majalisar zartarwa, Ahmed Lawan (APC-Yobe) ciyaman na kwamitin majalisar wakilai don bayyanawa jama’a hasashen majalisar wanda ya sabawa ra’ayin ‘yan Najeriya

- Lawan yace kwamitin anyishi ne don hada wani taro mai lakabin “Open Week” don wayar da kan mutane game da ayyukan majalisar a tsarin doka

- Lawan yace shirin ya kasance wani sabon cigaba da aka samu na Karin kusanci ga ‘Yan majalisar da mutanen da suke wakilta

An ba jigon majalisar zartarwa, Ahmed Lawan (APC-Yobe) ciyaman na kwamitin majalisar wakilai don bayyanawa jama’a hasashen majalisar wanda ya sabawa ra’ayin ‘yan Najeriya.

Lawan yace kwamitin anyishi ne don hada wani taro mai lakabin “Open Week” don wayar da kan mutane game da ayyukan majalisar a tsarin doka.

Lawan yace shirin ya kasance wani sabon cigaba da aka samu na Karin kusanci ga ‘Yan majalisar da mutanen da suke wakilta, “zai kasance wata kafa wadda mutane zasu ringa tattaunawa da ‘Yan Majalisa masu wakiltar mazabarsu game da ayyukansu a tsarin doka.

KU KARANTA KUMA: Babu sa'ata a matan Kannywood - Jamila Nagudu

“Open Week zai fadakar da mutane ayyukan da suka kamata ace majalisar nayi, wanda muhimmi ciki shine doka, wakilci, da kuma sanar da mutane duk wasu ayyuka na ma’aikatun gwamnatin tarayya”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel