Yanzu Yanzu: Gwamnonin APC sun yasar da Oyegun, sunyi biyayya ga Buhari

Yanzu Yanzu: Gwamnonin APC sun yasar da Oyegun, sunyi biyayya ga Buhari

Dukannin gwamnonin APC 24 sun amince da fadin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa ya kamata a mutuntuta kundin tsarin jam’iyyar wajen zabar sababbin shugabanni na jam’iyyar.

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a yau bayan shugaba Buhari ya gana da wasu gwamnoni.

A makon da ya gabata wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, shugaba Buari ya kaddamar da tsawaita wa’adin shugabancin John Odigie-Oyegun a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Yanzu Yanzu: Gwamnonin APC sun yasar da Oyegun, sunyi biyayya ga Buhari

Yanzu Yanzu: Gwamnonin APC sun yasar da Oyegun, sunyi biyayya ga Buhari

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kuma dai, wani sanatan Najeriya ya sake mutuwa

Yari yace: “Mun tuntubi dukannin gwamnonin APC 24 sannan kuma bakin su yazo daya da na shugaban kasa cewa ya zama dole mu mutunta kundin tsarin jam’iyyar, zamu mutuntuna kundin tsarin mulkin tarayyan Najeriya. Don haka, mun amince da cewa za’a samu sauyi a dukkan mataki daga kananan hukumomi, jihohi da kuma kasa baki daya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel