Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: Buhari ya soke zaman majalisa ya gana da shugabannin tsaro

Yanzu Yanzu: Buhari ya soke zaman majalisa ya gana da shugabannin tsaro

Rahotanni sun kawo cewa an soke zaman majalisa na yau Laraba, 4 ga watan Afrilu.

A maimaikon haka shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro da misalin karfe 12:00 na rana.

Zuwa yanzu ba’a bayyana dalilin ganawar shugaban kasar da shugabannin tsaro ba, amma majiyoyi sun nuna cewa babu mamaki akwai dalilin gaggawa tunda yake akan yi ganawar tsaro ne a ranakun Litinin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kuma dai, wani sanatan Najeriya ya sake mutuwa

A baya shugaban kasar ya sha alwashin hukunta shugabannin tsaro idan aka sake samun lamari irin na sace yan matan Dapchi a ko wani yankin na kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel