Nigerian news All categories All tags
Caccakar Buhari: Orji Kalu ya mayar wa da Obasanjo martani mai zafi

Caccakar Buhari: Orji Kalu ya mayar wa da Obasanjo martani mai zafi

- Ba tabbas in aka zabi wani sabon shugaban ya dora inda Buhari ya tsaya

Tsohon gwamnan Jihar Abia, Dr Orji Uzor Kalu, ya mayar wa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, martani mai zafi, bisa sukar da yake yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. In da ya ce, Buhari yayi rawar ganin da ta kamata a sake zabarsa a karo na biyu domin karasa aikin alherin da ya faro.

Da yake jawabi yayin ziyarar da ya kaiwa babban basaraken yankin Egba, a fadarsa dake garin Alake a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, Ya ce “A dimukuradiyya dama ana samun masu goyan baya da kuma masu suka. Kamar yadda muke goyon bayan Buhari shi kuma Obasanjo yana kushe sa.”

Caccakar Buhari: An mayar wa da Obasanjo martani mai zafi

Caccakar Buhari: An mayar wa da Obasanjo martani mai zafi

Jawabinsa nasa dai yazo ne, a dai-dai gabar da gwamnatin shugaba Muhammadu ke fuskantar matsananciyar suka daga tsoffin shugabannin kasar nan, kamar Ibrahim Badamasi Babangida da ma shi kansa Obasanjon, inda suke nuni da gazawarsa da kuma rashin cancantar sake zabarsa a kakar zabe mai zuwa ta 2019.

A cewar sarkin “Tabbas shugaba Bauhari ya cancanci ya kara darewa karagar mulkin Najeriya, domin irin aiyukan cigaba da ya yake yi” duk da dimbin kalubalan da yake fuskanta.

“Babbar matsalarmu a kasar nan ita ce, rashin samun shugabanni na gari ba mabiya ba, shuwagabannin da zasu bi doka da oda su kuma sanya al’umma a gabansu.

A baya mun yi shugabanni a kasar nan, da suke bin son ransu ba tare da bin doka ba. Suka yi yadda ransu yake so, amma yanzu su ne suke fadar maganganu iri-iri tare da kushe duk abinda wasu suka yi. "Burinmu shi ne hadin kan Najeriya domin ba abu ne da sai an shawarci wani ba.”

KU KARANTA: Babu sa'ata a matan Kannywood - Jamila Nagudu

Ana sa jawabin, Sarki (Oba) Gbadebo, ya ce, tabbas shugabancin kasar nan na yanzu yana iyakar kokarinsa kuma yana sarai da fatan cewa Najeriya zata samu ci gaba sosai, kana ya bayyana Orji Kalu da cewa hazikin shugaba ne a lokacin da yake gwamnan Jihar Abia. Sannan yayi alkawarin ba shi dukkan gudunmawar da yake bukata idan bukatar hakan ya taso.

Basaraken ya kuma kara da, “Ni ma zan so a bashi (Muhammadu Bauhari) Karin wata damar domin haka zai zamto tamkar kyankyashe kwayayen da ya dasa ne.”

Caccakar Buhari: An mayar wa da Obasanjo martani mai zafi

Caccakar Buhari: An mayar wa da Obasanjo martani mai zafi

"Yanzu da zarar wani ne ya hau, sai ka ga yayi fatali da kyawawan manufofi da aiyukan da ya faro, domin kada ya karasa a ce ai na tsohon shugaban kasa ne.” Kana daga bisani yayi masa fatan alheri a zagayen da Kalun yake na ganin Muhammadu Buhari ya sake zama shugaban kasa a 2019.

Daga karshe, Kalu ya kuma jaddada godiyarsa da irin gudunmawar da basaraken yake bayar wa, wajen tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel