Nigerian news All categories All tags
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC yau

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC yau

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ganawa da wasu gwamnonin jami’iyyar All Progressives Congress APC yau Laraba, 4 ga watan Afrilu, 2018 a kan rikicin cikin gidan da ke faruwa a jam’iyyar.

Buhari ya gana da su ne bayan rashin jituwa da aka samu tsakanin gwamnoni jiya a ganawar da akayi a fadar shugaban kasa.

Gwamnoni biyar ne suka gana da shi yau. Daga cikinsu sune gwamnan jihar Imo, Rochas okorocha; gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC yau

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC yau

Wadannan gwamnoni biyar ne suka nuna goyon bayansu ga shugaba Buhari kan rashin amincewa da kara wa’adin shugabancin John Oyegun.

Shugaba Buhari ya gana da dukkan gwamnonin jam'iyyar APC a jiya domin tattaunawa kan magance rikicin da ke huro wuta a jam'iyyar kafin zaben 2019 ya karaso. Amma ba'a samu kawo maslaha ba yayinda akayi baran-baran tsakanin juna.

KU KARANTA: Dalilin da yasa muka caccaki Buhari a babban masallacin tarayya – Yan Shi’a

Jam'iyyar APC dai ta kara wa'adin shugabancin John Oyegun, amma wasu kusoshi a jam'iyyar sun tayar da jijiyar wuya kan wannan abu kuma sun siffantashi a matsayin abinda ka iya janyo faduwar jam'iyyar a 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel