Nigerian news All categories All tags
Jami'ar Bayero zata bude gidajen talabijin da rediyo

Jami'ar Bayero zata bude gidajen talabijin da rediyo

- Mohammad Yahuza Bello, shugaban jami’ar Bayero, kano, yace jami’ar na kokarin bude gidan radio da talabijin

- Farfesa Mohammad Bello ya bayyana haka a lokacin bikin yaye dalibai karo na 34

- Bello yace aikin kafa injinan gudanar da aikin ya kai wani matsayi na kusan karshe, kuma jami’ar ta samu izinin watsa labaru na gidan radiyon ta

Shugaban jami’ar Bayero dake Kano, Mohammad Yahuza Bello, yace jami’ar na kokarin bude gidan radio da talabijin. Farfesa Mohammad Bello ya bayyana haka a lokacin bikin yaye dalibai karo na 34.

Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, Bello yace aikin kafa injinan gudanar da aikin ya kai wani matsayi na kusan karshe, kuma jami’ar ta samu izinin watsa labaru na gidan radiyon daga hukumar kula da watsa labarai na kasa (NBC).

Jami'ar Bayero zata bude gidajen talabijin da rediyo

Jami'ar Bayero zata bude gidajen talabijin da rediyo

DUBA WANNAN: Jerin kasashe 10 da sukafi yawan al'umma a nahiyar Afirka

Ya kara da cewa gidan talabijin din kuma zai fara aiki da zarar hukumar watsa labaru ta basu takardar izini.

A shekara 2017, jami’ar Legas ta zama jami’a ta farko da aka bawa takardar izinin bude gidan talabijin. A lokacin Ralph Akinfeleye, Ciyaman na gidan radiyo da talabijin na jami’ar Legas, yace jami’ar ta kasance ta farko a Afirika da aka bawa izinin bude gidan talabijin a cikin makaranta.

Legit.ng ta ruwaito cewa Farfesa Bello, yace za’a bawa dalibai 72 Digiri na matakin farko a wannan shekarar. Ya bayyana hakane a ranar Litinin 26 ga watan Maris, lokacinda yake zantawa da manema labarai. Ya kara da cewa zasu yaye dalibai 8,635, a wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel