Shugaba Buhari yasa a binciko barnar da akayi a jihohin da rikicin manoma da makiyaya ya shafa

Shugaba Buhari yasa a binciko barnar da akayi a jihohin da rikicin manoma da makiyaya ya shafa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurni ga hukumar bayar da taimakon gaggawa data fara bincike a kan barnar da akayi a garuruwan da rikicin ya shafa

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka lokacin kaddamar da kungiyar gwamnati a fadar shugaban kasa

- Shugaban kasar ya bayar da umurnin binciken ne saboda a samar wa garuruwan tallafi don sake ginasu da karfafawa al'ummar jihohin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurni ga hukumar bayar da taimakon gaggawa data fara bincike akan barnar da akayi a garuruwan da rikicin ya shafa na makiyaya da manoma, a fadin Najeriya.

Shugaba Buhari yasa a binciko barnar da akayi a jihohin da rikicin manoma da makiyaya ya shafa

Shugaba Buhari yasa a binciko barnar da akayi a jihohin da rikicin manoma da makiyaya ya shafa

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana haka lokacin kaddamar da kungiyar gwamnati a fadar shugaban kasa. Yemi Osinbajo yace, “Shugaban kasa ya bayar da umurnin cewa muyi bincike a kan barnar da aka yiwa garuruwan da rikicin manoma da makiyaya ya shafa a fadin kasar nan”.

DUBA WANNAN: Yadda wani fasto ya kashe budurwarsa kuma ya binne ta a haraban coci

Wasu daga cikin garuruwan da rikicin yafi shafa sun hada da jihar Binuwai, Plateau, Taraba, Zamfara, Oyo, Kogi, Ekiti, da Ondo. Osinbajo a ranar 15 ga watan Fabrairu, ya bayyanawa kungiyar tattalin arziki, cewa Buhari ya bayar da umurnin kafa kwamitin na sake gina garuruwan da rikicin ya shafa.

Mataimakin mai bayar da shawara ta fannin yada labarai, Mr Laolu Akande, da mataimakin shugaban kasa sune suka jagoranci taron. Inda mataimakin shugaban kasar yayi kira ga kungiyar ta NEMA dasu hada kai da masu ruwa da tsaki a cikin al’amuransu tare da kungiyoyi masu zaman kansu.

Bayan haka mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, a ranar Talata, ya karbi bakuncin kungiyar kasuwanci daga Jami’ar ta Oxford a kasar Ingila, a fadar shugaban kasa, wadda Mr Bayo Owolabi ya jagoranta. Kungiyar tayi godiya ga mataimakin shugaban kasar bisa ga yanda Najeriya ta kara bunkasa a fannin kasuwanci a bankin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel