Nigerian news All categories All tags
Za’a gurfanar da Dino Melaye tare da yan bindiga 4 ranan 10 ga Mayu

Za’a gurfanar da Dino Melaye tare da yan bindiga 4 ranan 10 ga Mayu

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta gurfanar da Sanata Dino Melaye tare da yan bindigan 4 kan laifin mallakan muggan makamai a babban kotun tarayya da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi ranan 10 ga watan Mayu, 2018.

Yan bindigan sune Kabiru Seidu Osama, Nuhu Salisu, 25, Musa Mohammed, 27, da Emmanuel Audu, 26.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa ranan 28 ga watan Maris, hukumar yan sandan jihar Kogi ta alanta arcewa yan baranda 6 daga kurkukunta da ke jihar Kogi.

Hakazalika ranan 30 ga watan Maris, Legit.ng ta kawo muku cewa hukumar ta alanta nasaran damko dukkan wadanda suke arce.

Za’a gurfanar da Dino Melaye tare da yan bindiga 4 ranan 10 ga Mayu

Za’a gurfanar da Dino Melaye tare da yan bindiga 4 ranan 10 ga Mayu

Kakakin hukumar yan sandan, ACP Jimoh Moshood, wanda ya yi wanan bayani a hira da manema labarai ya bayyana cewa an damke Seidu ne a karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi. Shi kuma Salisu a kauyen Ganaja, jihar Kogi.

KU KARANTA: Sabbin masana'antun wutar lantarki 4 za su fara aiki gadan-gadan a Najeriya

Sauran da aka damke sune John Beneche, 22, Seye Atowoju, 27 Danjuma Yunusa, 35 , Egga Ochai,50 Abbas Haruna, 30 da Gloria Audu, 28.

Zaku tuna cewa Seidu ya bayyanawa hukuman yayin bincike cewa Sanata Dino Melaye ya bashi bindigogi da kudi N430,000.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel