Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin Tarayya ta na shirin tsare-tsaren dakatar da kashe-kashe a Birnin Gwari - Dambazzau

Gwamnatin Tarayya ta na shirin tsare-tsaren dakatar da kashe-kashe a Birnin Gwari - Dambazzau

A ranar Talata 3 ga watan Afrilu, Jaridar Legit.ng ta samu rahoto da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa, gwamnatin tarayya da fara gudanar da wasu tsare-tsare domin kawo karshen kashe-kashe a garin Birnin-Gwari na jihar Kaduna.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau shine ya bayyana hakan a ranar Talatar da gabata da cewa, wannan cin kashi ya kai makura a mahanga ta gwamnatin tarayya.

Abdulrahman Dambazzau

Abdulrahman Dambazzau

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da ya kaiwa mai martaba Sarkin Birnin-Gwari, Malam Zubairu Jibril Maigwari, inda yake cewa wannan lamari na kashe-kashe, garkuwa da mutane tare da ta'addanci na sace-sacen shanu a garin ya kai makura.

KARANTA KUMA: Jerin sunayen manyan Kabilu da jihohin su a Najeriya

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, 'yan tawagar ministan sun hadar da; mataimakin shugaban 'yan sanda, Mista Habila Joshak tare da kwamishinan 'yan sanda na jihar Kaduna, Mista Austin Iwar.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an kashe dakarun soji 11 a yankin na Birnin Gwari tun a ranar 20 ga watan Maris, inda kuma akayi garkuwa da wasu mutane 9 da suka hadar da wata gallaleyiyar amarya tare kawaye masu rakiyarta dakin miji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel