Nigerian news All categories All tags
Obasanjo bai cancanci ya zargi kowa ba akan cin hanci da rashawa - Ayo Adebanjo

Obasanjo bai cancanci ya zargi kowa ba akan cin hanci da rashawa - Ayo Adebanjo

- Jigon Afenifere, Ayo Adebanjo yace tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo bashi da hurumin zargin wani da aikataa cin hanci da rashawa

- Ya bayyana Obasanjo a matsayin farar mage, Adebanjo yace Obasanjo N20,000 kadai yake da ita a asusun ajiyarsa na banki lokacin da ya fito daga gidan yari a shekarar 1999

- Adebanjo yace inda najeriya kasace ta mutane masu tinani da Obasanjo bai kara shiga cikin al’amuran rayuwar mutanen kasar nan

Jigon Afenifere, Ayo Adebanjo yace tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo bashi da hurumin zargin wani da aikataa cin hanci da rashawa a kasar nan.

Ya bayyana Obasanjo a matsayin farar mage, Adebanjo yace Obasanjo N20,000 kadai yake da ita a asusun ajiyarsa na banki lokacin da ya fito daga gidan yari a shekarar 1999, sai tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar da wani mashahurin dan kasuwa, Oyewole Fasawa ne suka hana ya talauce.

Obasanjo bai cancanci ya zargi kowa ba akan cin hanci da rashawa - Ayo Adebanjo

Obasanjo bai cancanci ya zargi kowa ba akan cin hanci da rashawa - Ayo Adebanjo

Adebanjo yace inda najeriya kasace ta mutane masu tinani da Obasanjo bai kara shiga cikin al’amuran rayuwar mutanen kasar nan, amma ina mamaki yanda har yanzu mutane suke masa wani kallo na mutumin kirki duk da sanin halayensa.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar ANN sun hada kai da Obasanjo wajen adawa da Buhari a zaben 2019

Ayo Adebanjo wanda zai cika shekaru 90 a ranar 10 ga watan Afirilu, a labarin da yake bayarwa na rayuwarsa wanda ya aka gabatar a ranar Talata a jihar Legas, wanda ya hada manyan mutanen kasar nan tare, inda ya bayyana gwamantin Obasajanjo daga 1999 zuwa 2007 a matsayin gwamnatin farar hula mara amfani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel