Nigerian news All categories All tags
Yadda wani fasto ya kashe budurwarsa kuma ya binne ta a haraban coci

Yadda wani fasto ya kashe budurwarsa kuma ya binne ta a haraban coci

- Hukumar ‘Yan Sanda ta kama wani fasto da ake tuhuma da kashe budurwarsa da kuma binneta a cikin cocinsa

- Kwamishinan ‘Yan Sanda Ahmed Iliyasu, yace hukumar ta samu rahoton bacewar wata a helikwatar ofishinsu

- Kwamishinan yace hukumar ta samu rahoton ne, daga gurin wani Adebola Saheed

A ranar 3 ga watan Afirilu, 2018, a Ewekoro jihar Ogun, Hukumar ‘Yan Sanda ta jihar, ta kama wani fasto da ake tuhuma da kashe budurwarsa da kuma binneta a cikin cocinsa mai suna Holy gathering Evangelical Church of God bayan ya cire wasu sassan jikinta don yin tsafi.

Yadda wani fasto ya kashe wata mata kuma ya binne ta a haraban coci

Yadda wani fasto ya kashe wata mata kuma ya binne ta a haraban coci

Kamar yadda yan sandan suka bayyana faston ya kashe matar ne kuma ya file kanta da hannuwa da wasu sassan jikin ta kafin ya binne ta a wani daki da ke harabar cocin nasa. Matar mai suna Raliat Sanni dai bazawara ce kuma tana sana'ar gyaran gashi.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Ahmed Iliyasu, yace hukumar ta samu rahoton bacewar wata a hedikwatar ofishinsu dake Ewekoro. Kwamishinan yace hukumar ta samu rahoton ne, daga gurin wani Adebola Saheed, wanda yace kanwarsa, Mrs Raliat Sanni mai shekaru 35, ta bar gida tun 21 ga watan Maris amma bata dawo ba.

KU KARANTA: Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta

Iliyasu yace bayan samun rahoton jami’an tsaron suka shiga bincike wanda, SP Oluwarotimi Jere, ya jagoranta, inda suka gano cewa faston shine mutum na karshe da aka gani tare da Raliat. Bayan an kamoshi an gudanar da bincike ya amsa laifinsa.

A lokacin da ake bincikensa ya bayyana cewa ya kasheta kuma ya binneta a cikin cocinsa bayan ya cire mata kai da hannaye biyu, bisa ga dalilan da bai bayyana ba.

Ya kuma fadi sunan wanda suka aikata ta’adin tare, inda shima akayi nasarar kamashi, duk da dai ya karyata Faston yace rabonsa dasu hadu tun bara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel