Nigerian news All categories All tags
Jam’iyyar ANN sun hada kai da Obasanjo wajen adawa da Buhari a zaben 2019

Jam’iyyar ANN sun hada kai da Obasanjo wajen adawa da Buhari a zaben 2019

- Yayin da guguwar zabe na 2019 ke kara tasowa jam’iyyar ANN sun hada kai da tsohon shugaban kasa Obasanjo da wasu mutane wurin adawa da shugaba Buhari

- Obasanjo ya soki Buhari a lokacin da kungiyar matasa suka kai masa ziyara a karshen satin daya gabata

- Ciyaman na kungiyar jagorancin jam’iyyar ANN, Adekoya Adebolaya nuna goyon baya bisa ga jawaban da tsahon shugaban kasar yayi na cewa zaben 2019 lokacin ne na tantance kwazon ba wai suka ga gwamnatin data shude ba

Yayin da guguwar zabe na 2019 ke kara tasowa jam’iyyar ANN sun hada kai da tsohon shugaban kasa Obasanjo da wasu mutane wurin adawa da shugaba Buhari.

Obasanjo ya soki Buhari a lokacin da kungiyar matasa suka kai masa ziyara a karshen satin daya gabata.

Ciyaman na kungiyar jagorancin jam’iyyar ANN, Adekoya Adebolaya nuna goyon baya bisa ga jawaban da tsahon shugaban kasar yayi na cewa zaben 2019 lokacin ne na tantance kwazon ba wai suka ga gwamnatin data shude ba.

Ya buhakaci ‘yan Najeriya dasu fito kwai da kwalkwata lokacin zabe na 2019, don kawan da wannan gwamnatin data kasa ta APC da Shugaba Buhari daga kan mulki. Yace jam’iyyarsu ta ANN a shirye take data tsayar da dan takara jajirtacce wanda zai jagoranci Najeriya cikin adalci.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan siyasan da ka iya kawowa Shugaba Buhari cikas a zaben 2019

Ya kuma bukace ko wane dan Najeriya da ya tabbatar yayi katin zabe kafin lokacin yazo, ya kuma tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyarsu cike take da mutane maza da mata masu gaskiya da rukon amana, wanda zasu kawo cigaba a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel