Nigerian news All categories All tags
Rikita-Rikita: An fara shire-shiren yi wa Sanatocin jihar Kaduna kiranye

Rikita-Rikita: An fara shire-shiren yi wa Sanatocin jihar Kaduna kiranye

Wasu matasa a jihar Kaduna da suka ce suna rajin kare talaka da kuma matukar damuwa da jihar a karkashin inuwar kungiyar Kaduna Concerned Citizens ta ayyana cewa 'ya'yan ta tuni suka fara shire-shiren yi wa 'yan majalisar dattawan jihar kiranye.

Kamar dai yadda suka bayyana cewa sun fara hakan ne sakamakon korafe-korafe da kuma goyon bayan da suka samu daga al'ummar jihar musamman ma dai ganin cewa Sanatocin a cewar su ba su kaunar jihar ko kadan musamman ma ganin yadda suka hakan jihar cin bashin $ miliyan 350 daga bankin duniya.

Rikita-Rikita: An fara shire-shiren yi wa Sanatocin jihar Kaduna kiranye

Rikita-Rikita: An fara shire-shiren yi wa Sanatocin jihar Kaduna kiranye

KU KARANTA: Zaben 2019: Yadda zan kawo karshen rikicin Najeriya

Legit.ng ta samu cewa shugabannin kungiyar ne dai suka tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talatar da ta gabata yayin wani taron manema labarai da suka gudanar.

A wani labarin kuma, Yayin da shirye-shire ke ta dada kara kankama game da zabukan kananan hukumomin jihar Nasarawa dake a shiyyar Arewa ta tsakiya a wata mai kamawa, da alamu kawunan masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC mai mulki a jihar sun rabu.

Mun samu dai cewa jiga-jigan jam'iyyar ta APC a jihar dai tuni suka kai kukan su gaban gwamnan jihar inda suka roke shi da ya duba girman Allah kar ya kakaba masu shugabannin da ba su so a kananan hukumomin na.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel