Ya rataye kansa bayan dawowa daga Islamiyya

Ya rataye kansa bayan dawowa daga Islamiyya

- A satin da muke ciki ne wata matashiya ta kashe kanta bayan da ta sha fiya-fiya

- kafin kashe kan nasa, Al'amin ya kauracewa wasa da yan uwansa yara.

Wani yaro mai suna Muhammad Al'amin, ya rataye kansa da igiya har lahira, a Jihar Gombe. Rundunar yan sanda ta Jihar ta tabbatar da faruwar al'amarin, da take bayyana yadda lamarin ya faru, jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, Mary Malum, ta ce "an gano gawar Yaron ne da misalin karfe hudu na yamma (4:00 pm), a ranar Litinin."

Ya rataye kansa bayan dawowa daga Islamiyya

Ya rataye kansa bayan dawowa daga Islamiyya

Mahaifin Yaron wanda Jami'in dan sanda ne Insp. Abdu Manu wanda dake aiki tare da sashin bincike na ofishin rundunar na garin Pantami, ya ce, matarsa ce ta kira shi a waya ta shaida masa cewa an ga gawar dan nasu mai shekaru 13 a cikin dakinsa bayan dawowarsa daga makarantar islamiyya.

Mary Malum ta ce, bayan da suka sami labarin ne, muka tura jami'an yan sanda nan take don daukar hotunan yaron da wurin da kuma yadda abin ya faru. Ta kuma kara da cewa,

KU KARANTA: Jam’iyyar ANN sun hada kai da Obasanjo wajen adawa da Buhari a zaben 2019

Yanzu haka an samu igiyar da yayi amfani da ita da kuma gawar yaron wadda yanzu haka aka kai ta sashin ajiyar gawa na babban Asibitin Gombe, domin zurfafa bincike.

Mary ta kuma ce, , "har ya zuwa yanzu muna kan binciken yadda lamarin ya faru kuma da zarar an samu wani karin haske rundunar zata shaidawa manema labarai."

Sai dai wasu yara yan unguwar da iftila'in ya afku, sun shaidawa majiyarmu cewa, kafin kashe kan nasa, Al'amin ya kauracewa wasa da yan uwansa yara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel