Nigerian news All categories All tags
Buhari zai yi wani bulaguro na sirri zuwa birnin London sati mai zuwa

Buhari zai yi wani bulaguro na sirri zuwa birnin London sati mai zuwa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai wata ziyarar kashin kansa zuwa Landan sati mai zuwa

- Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya ki cewa a kan ziyarar, da aka tuntube shi

- A shekarar da ta gabata, shugaba Buhari, ya shafe watanni da dama yana zaman jinya a birnin Landan na kasar Ingila

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai wata ziyarar kashin kansa zuwa birnin Landan dake kasar Ingila a nahiyar Turai, ranar Litinin mai zuwa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, wata majiya ce daga fadar shugaban kasa ta tabbatar mata da hakan a jiya.

Buhari zai yi wani bulaguro na sirri zuwa birnin London sati mai zuwa

Buhari zai yi wani bulaguro na sirri zuwa birnin London sati mai zuwa

Majiyar, da jaridar ta ce bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce shugaba Buhari zai je birnin na Landan ne domin wasu uzuri na kashi kansa

Saidai bai sanar da jaridar yanayin irin wadannan bukatu da zasu kai Buhari Landan din ba.

Shugabannin kasashen common wealth, da suka hada da Najeriya, (CHOGM) zasu yi taro a birnin na Landan, amma sai ranakun 15 da 20 ga wata.

DUBA WANNAN: Dan jami'in dan sanda ya rataye kansa a jihar Gombe

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ki cewa komai a kan batun ziyarar da jaridar Daily Trust ta tuntube shi.

A shekarar da ta gabata, shugaba Buhari, ya shafe watanni masu tsawo yana zaman jinya a kasar ta Ingila.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel