Nigerian news All categories All tags
Wani babban Limami ya hallaka budurwasa, ya binne gawarta a dakin bautansa

Wani babban Limami ya hallaka budurwasa, ya binne gawarta a dakin bautansa

Rundunar Yansandan jihar Ogun ta samu nasarar cafke wani babban Limamin Coci wanda take zargi da kashe budurwarsa tare da binne gawarta a cikin Cocinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Kwamishinan Yansandan jihar, Ahmed Iliyasu ne ya bayyana haka a ranar Talata 3 ga watan AFrilu, inda yace sun samu korafi daga wani matashi Adebola Saheed, wanda yace kanwarsa, Raliat Sanni ta bace tun ranar 21 ga watan Maris da ta fita bata dawo gida ba.

KU KARANTA: Daukar fansa: Sojojin Najeriya sun yi masu yan bindiga luguden wuta a Kaduna

The Cables ta ruwaito Iliyasu yana cewa bayan samun karar sai Yansanda suka bazama suka kaddamar da bincike, inda suka gano Faston ne mutum na karshe da Raliat ta hadu da shi kafin bacewarta, ba tare da wata wata ba, Yansanda suka yi ram da shi.

“Bayan mun fara tambayarsa, Faston ya bayyana mana cewar ya kashe Raliat, inda ya cire mata kai da hannuwanta, sa’annan ya binne gangar jikin a Cocinsa. Wannan mugunta ne, babban abin bakin cikin shine ashe Raliat buduwarsa ce, a boye.” Inji Kwamishinan.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Faston yana cewa gaskya bashi ya kashe Raliat ba, inda ya kara da cewa wani abokin aikinsa ne ya aikata wannan ta’asa ga Raliat, amma fa da umarninsa, inda suka yanke mata kai da hannuwa, don cika umarnin kungiyarsu ta asiri.

Sai dai shi ma abokin aikin Faston wanda tuni Yansanda suka cika hannu da shi ya musanta zargin da Faston yayi masa, inda yace rabonsa da ganin Faston ya haura shekara daya ma. Daga karshe Kwamishinan yace zasu gurfanar da su gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel