Nigerian news All categories All tags
Ta zarce ko ta lankwashe: An tashi baram baram a tsakanin Buhari da Gwamnonin jam’iyyar APC

Ta zarce ko ta lankwashe: An tashi baram baram a tsakanin Buhari da Gwamnonin jam’iyyar APC

Kememe Gwamnonin jam’iyyar APC sun ki yarda su yi karin haske game da ganawar da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Villa, a ranar Talata 3 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito gwamnonin sun sanya ma bakunansu linzami ne duk da kwashe sama da awa guda suna tattaunawa da Buharin, sai dai wata majiya ta karkashin kasa ta shaida ma majiyar Legit.ng cewar an kasa samun matsaya ne tsakanin Buhari da Gwamnonin.

KU KARANTA: Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi raddi game da batun gano akwati cike da daloli makil a gidansa

Har aka kammala taron, gwamnonin da Buharin sun kasa shawo kan kalubalen dake fuskantar jam’iyyar, musamman wanda ya shafi wa’adin mulkin shuwagabannin jam’iyyar, duk da cewa sai da gwamnonin suka fara tattaunawa a tsakaninsu kafin su gana da Buhari.

Ta zarce ko ta lankwashe: An tashi baram baram a tsakanin Buhari da Gwamnonin jam’iyyar APC

Buhari da Gwamnonin jam’iyyar APC

Idan za’a tuna, a ranar 27 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haramcin cigaba da rike madafan iko ga shuwagabannin APC, wanda hakan na nufin Buharin ya janye kalaman da yayi a taron jam’iyyar na baya, inda ya bukaci shuwagabannin su zarce na tsawon shekara daya.

Sai dai majiyar ta kara da cewa da alama gwamnonin zasu sake ganawa da Buhari a sati mai zuwa don karkare tattaunawar da suka fara, musamman duba da rarrabuwar kai da aka samu a tsakaninsu game da wa’adin mulkin shuwagabannin jam’iyyar, ta zarce ko ta lankwashe.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da Yahaya Bello na Kogi, Jibrilla Bindow na Adamawa, Abubakar Badaru Jigawa, Rauf Aregbesola Osun, Atiku Bagudu Kebbi, Rotimi Akeredolu Ondo, Abdulfatah Ahmed Kwara,

Godwin Obaseki (Edo), Abdullahi Ganduje (Kano), Tanko Al- Makura (Nasarawa), Kashim Shettima (Borno), Rochas Okorocha (Imo), Akinwunmi Ambode (Lagos), Abiola Ajimobi (Oyo), Abubakar Bello (Niger), Aminu Tambuwal (Sokoto), Abdulaziz Yari (Zamfara), Simon Lalong (Plateau), Samuel Ortom (Benue), Nasir El-Rufai (Kaduna) da Ibikunle Amosun (Ogun).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel