Nigerian news All categories All tags
Jerin barayi: Sanatan APC ya caccaki Gwamnatin Shugaba Buhari

Jerin barayi: Sanatan APC ya caccaki Gwamnatin Shugaba Buhari

- Sanata Shehu Sani yayi magana game da sunayen barayi da aka fitar

- Kwamared Shehu Sani ya nuna cewa saura barayin cikin gida na APC

- Gwamnatin Buhari ba ta dai kawo ‘Yan Jam’iyyar APC cikin barayin ba

Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Kwamred Shehu Sani ya tofa albarkacin bakin sa game da sunayen wasu barayin kasar nan da aka fitar a karshen makon da ya wuce.

Jerin barayi: Sanatan APC ya caccaki Gwamnatin Shugaba Buhari

Babu 'Yan Jam’iyyar APC cikin wanda su ka saci kudi

Shehu Sani wanda shi ne Shugaban kwamitin bashi a Majalisar Dattawa yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda yace manyan Jam'iyyun kasar sun nishadantar da Jama'a da jerin sunayen da su ka fitar na wanda su ka saci kudi.

KU KARANTA: Mutane 3 da aka sunan su cikin barayin Najeriya sun fitar da kan su

Abin da ya rage shi ne yanzu Gwamnatin Shugaba Buhari ta fitar da sunayen Waliyyan kasar wanda ba su taba satar ko kobo na dukiyar Jama'a ba inji Sani. Sanatan dai yana nufin a bayyana wadanda su ka saci kudin Gwamnati a APC.

Ministan yada labarai da al'adu Lai Mohammed ya fitar da jerin wanda su ka saci kudin Najeriya wanda duk 'Yan PDP ne. Su ma dai Jam'iyyar adawa sun yi wuf sun fitar da sunayen wasu manyan 'Yan APC da su ka ce duk barayin ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel