Nigerian news All categories All tags
Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi raddi game da batun gano akwati cike da daloli makil a gidansa

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi raddi game da batun gano akwati cike da daloli makil a gidansa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya musanta rahoton da ake yadawa a shafukan sadarwar zamani dake cewa an gano wasu makudan dalolin Amurka cike da wani akwati a gidansa.

Daily Trust ta ruwaito Kaakakin Jonathan, Reno Omokri ne ya bayyana haka, inda yace ba gaskiya bane wani bidiyon da ake yadawa dake nuna Yansanda sun kai samame gidan Jonathan, wai har sun gano akwatin daloli.

KU KARANTA: Na fi kaunar mutanen da za su faɗa min gaskiya komai ɗacinta– Masari ga hadimansa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa: “Mu sani babu wasu Yansanda ko wasu jami’an tsaro da suka kai samame gidan Jonathan, kuma babu wasu kudaden kasashen waje da aka gano a gidansa.”

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi raddi game da batun gano akwati cike da daloli makil a gidansa

Hoton da ake yadawa

Sai dai Reno ya tabbatar da cewar wasu barayi sun yi sata a gidan Jonathan a shekarar 2017, amma ko a lokacin basu saci kudi ba, illa na’rorin wuta da suka dauke. Kaakakin yace duk wasu abubuwan da Jonathan ya mallaka ya same su ne ta halastacciyar hanya.

Daga karshe ya shawarci jama’a da su dinga kula da irin labaran da suke karantawa a shafukan sadawar zamani, musamman masu yin batanci ga shugaba Jonathan, inda ya danganta labaran ga masu nufin nata ma Jonathan suna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel