2019: Abubuwan da za su iya kawowa Kwankwaso cikas na mulkin Najeriya

2019: Abubuwan da za su iya kawowa Kwankwaso cikas na mulkin Najeriya

Wannan karo mun shiga fagen siyasa inda mu ka kawo maku wasu dalilan da za su iya kawowa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso matsala wajen yunkurin da yake kokarin yi na tsayawa takarar Shugaban kasa ko da irin kokarin da yayi a 2014.

Duk da Sanatan bai bayyana nufin sa ba amma ga abubuwan da za su iya kawo masa tasgaro:

2019: Abubuwan da za su iya kawowa Kwankwaso cikas na mulkin Najeriya

‘Yan Kwankwasiyya su na ganin ba ayi da su a APC

1. Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC

Zai yi wahala a samu wani a cikin Jam’iyyar APC mai mulki da zai iya tika Shugaban kasa Buhari da kasa a zaben fitar da gwani. Da ace Kwankwaso yana wata Jam’iyyar ne da kila ya fi samun damar karawa da Shugaba Buhari.

KU KARANTA: An gano wanda ya zamewa Atiku matsala a lamarin siyasa

2. Rikicin tsohon Gwamnan da Ganduje

2019: Abubuwan da za su iya kawowa Kwankwaso cikas na mulkin Najeriya

Gwamna Ganduje yana tare da Shugaba Buhari

Rigimar Rabiu Musa Kwankwaso da Magajin sa Ganduje na iya cin shi idan ya fito takara a 2019. Ba shakka Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje za tayi kokari fallasa abin da Kwankwaso yayi a Gwamnatin sa da wasu ke kira aik-aika.

3. Sa-in-sa da rashin jituwa da sauran ‘Yan siyasa

Mu na da labari cewa duk da Kwankwaso yana cikin wadanda Talakawan Najeriya ke kauna a halin yanzu, sai dai Jagoran na Kwankwasiyya bai da alaka mai kyau da sauran manyan ‘yan siyasan kasar da wasu bangare na 'Yan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel