Nigerian news All categories All tags
Harkar tsaro: Idan Gwamnatin Buhari ta gaza a tsige ta – Ben Murray Bruce

Harkar tsaro: Idan Gwamnatin Buhari ta gaza a tsige ta – Ben Murray Bruce

- Sanatan na Jihar Bayelsa yayi Allah-wadai da Gwamnatin Shugaba Buhari

- Sanata Ben M. Bruce yace a kullum jama’a na kokawa game da harkar tsaro

- ‘Dan Majalisar yace idan masu madafan iko ba za su iya ba su fice daga ofis

Sanata Ben Murray Bruce mai wakiltar Bayelsa a Majalisar Dattawa yayi Allah-wadai da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin matsalar da ake samu a sha’anin tsaro.

Harkar tsaro: Idan Gwamnati ta gaza a tsige ta – Ben Murray Bruce

Sanatan Bayelsa yayi Allah-wadai da Gwamnatin Buhari

Fitaccen Sanatan Jam’iyyar PDP ya koka da yadda Makiyaya da sauran wasu tsirarru ke fitinar jama’a a kasar nan. Ben Bruce yace lokaci yayi da za a nemi Sojoji su kawo karshen barnar da ake yi a Najeriya ko kuma a dauki mataki.

KU KARANTA: Obasanjo ya kuma sukar Buhari yace Gwamnatin sa ba ta da kan gado

‘Dan Majalisar yayi wannan jawabi ne a wani zaman Majalisa inda yace ya kamata Ministocin tsaro da Manyan Hafsoshin Jami’an tsaro su bar ofishin su idan ba za su iya magance matsalar ba domin abin na nema ya zama hauka.

Ben Bruce yake cewa idan Shugaban kasa Buhari ba zai yi maganin wannan matsalar ba yayi murabus ko kuma a tsige sa. Sanatan yace idan har babu wanda zai iya kawo karshen matsalar sai Bukola Saraki sai ya hau mulkin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel