Nigerian news All categories All tags
Dan jami'in dan sanda ya rataye kansa a jihar Gombe

Dan jami'in dan sanda ya rataye kansa a jihar Gombe

Wani yaro mai shekaru 13 kuma da ga wani jami'in dan sanda ya rataye kansa, kamar yadda hukumar ta sanar a yau.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Gombe, DSP Mary Malum, ta bayyana cewar an samu gawar yaron, Muhammadu Al-amin, rataye a dakinsa.

Malum ta ce, a ranar Litinin da misalin karfe 4:00 na yamma, mahaifin yaron, Inspekta Abdu Manu dake aiki da sashen binciken laifuka a ofishin 'yan sanda dake Pantami, ya samu kiran waya daga matar sa cewar an samu dansu mai shekaru 13 ya rataye kansa a dakinsa.

Dan jami'in dan sanda ya rataye kansa a jihar Gombe

Dan jami'in dan sanda ya rataye kansa a jihar Gombe

Malum ta kara da cewar, mahaifin yaron ya shigar da rahoton mutuwar yaron tare da bayyana cewar, yaron ya rataye kansa ne bayan dawowar sa daga makarantar islamiyya.

Kakakin ta ce, bayan samun rahoton, jami'an 'yan sanda sun ziyarci gidan su yaron kuma sun samu gawar sa da wasu ragowar igiyoyin da ya yi amfani da su. Hukumar 'yan sanda ta dauki hotuna sannan ta dauki gawar yaron ya zuwa asibitin kwararru dake Gombe domin gudanar da bincike a kan gawar.

DUBA WANNAN: An gano mutumin da ya zamar wa Atiku kadangaren bakin tulu a siyasa

Wani mazaunin unguwar da abin ya faru ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar, an ga yaron da rana yana wasa da abokansa kafin jim kadan su samu labarin cewar ya mutu.

Kokarin NAN na jin ta bakin mahaifin yaron bai kai ga nasara ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel