Zaben 2019: Sule Lamido ya ayyana yadda zai kawo karshen rikice-rikicen Najeriya

Zaben 2019: Sule Lamido ya ayyana yadda zai kawo karshen rikice-rikicen Najeriya

Fitaccen dan siyasar nan tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan kuma mai takarar neman tikitin takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2019 Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa ta wani bangaren kalaman shugaba Buhari ne ke haddasa ruruwar wutar rikicin kashe-kashen da ake fama da shi a Najeriya.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu ta Radiyo Faransa wadda kuma suka wallafa tare da watsawa a kafafen yada labaran su.

Zaben 2019: Sule Lamido ya ayyana yadda zai kawo karshen rikice-rikicen Najeriya

Zaben 2019: Sule Lamido ya ayyana yadda zai kawo karshen rikice-rikicen Najeriya

A cewar sa, a baya shekaru 16 da suka wuce akwai Najeriya amma kuma babu yawaitar irin wadannan kashe-kashen amma tun da shugaba Muhammadu Buhari ya shiga siyasa sai komai ya canza.

Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa shi a mulki ba abunda ake bukata irin adalci da mutunta juna, domin hakan ne kadai zai iya kawo dawamammen zaman lafiya.

A wani labarin kuma, Wata kungiya dake rajin tabbatar da mulkin adalci da kuma tabbatauwar Demokradiyya da kuma kare hakkin dan adam wadda ba ta gwamnati ba watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAF) a takaice ta yi kira ga 'yan majalisun tarayyar Najeriya da su gaggauta maida kudaden da suke ansa.

Wannan dai kamar yadda suka ce ya biyo bayan kwarmaton da Sanata Shehu Sani yayi inda ya fallasa cewa 'yan majalisar na dattawa na karbar akalla Naira miliyan 13 da rabi duk watan duniya domin gudanar da ayyukan yau-da-kullum.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel