Nigerian news All categories All tags
An bukaci Sanatoci da 'yan majalisar wakilai su maido kudaden haram din da suke ansa

An bukaci Sanatoci da 'yan majalisar wakilai su maido kudaden haram din da suke ansa

Kungiya dake rajin ganin tabbatar da mulki mai adalci da kuma tabbatauwar Demokradiyya da kuma kare hakkin dan adam wadda ba ta gwamnati ba watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yi kira ga 'yan majalisun tarayyar Najeriya da su gaggauta maida kudaden da suke ansa ba bisa ka'ida ba.

Wannan dai kamar yadda suka ce ya biyo bayan kwarmaton da Sanata Shehu Sani yayi inda ya fallasa cewa 'yan majalisar na dattawa na karbar akalla Naira miliyan 13 da rabi duk watan duniya domin gudanar da ayyukan yau-da-kullum.

An bukaci Sanatoci da 'yan majalisar wakilai su maido kudaden haram din da suke ansa

An bukaci Sanatoci da 'yan majalisar wakilai su maido kudaden haram din da suke ansa

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kashe sojin Najeriya 15

Legit.ng ta samu kuma cewa daga baya bayan matsin lamba sosai, hukumar da ke kula da kayyade alawus alawus din jami'an gwamnati ta bayyana cewa abun da ya kamata su rika ansa dai bai fi Naira miliyan 1 ba.

A wani labarin kuma, Wasu matasa a jihar Kaduna da suka ce suna rajin kare talaka da kuma matukar damuwa da jihar a karkashin inuwar kungiyar Kaduna Concerned Citizens ta ayyana cewa 'ya'yan ta tuni suka fara shire-shiren yi wa 'yan majalisar dattawan jihar kiranye.

Kamar dai yadda suka bayyana cewa sun fara hakan ne sakamakon korafe-korafe da kuma goyon bayan da suka samu daga al'ummar jihar musamman ma dai ganin cewa Sanatocin a cewar su ba su kaunar jihar ko kadan musamman ma ganin yadda suka hakan jihar cin bashin $ miliyan 350 daga bankin duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, to a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Haka ma, Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel